Ƙungiyoyin da suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Katsina da ke Najeriya na ta kiraye-kirayen sako jagororinsu, bayan da suka zargi jami’an tsaro da tsare su.
“Jami’an tsaron ne suka gayyaci jagororinmu domin su amsa wasu tambayoyi, sai dai tun bayan zuwansu sai aka tsare su, bisa zargin zuga wasu da ake zargi da aikata ba daidai ba a lokacin zanga-zangar,” in ji ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida yadda aka kama jagororin zanga-zangar.
Ya ce mutanen da jami’an tsaron ke tsare da su sun haɗa da: Shugaban ƙungiyar ‘Struggle for Good Governance’, Habibu Muktar Ruma, da sakataren ƙungiyar ‘Coalition for Civil Society’, Kwamared Kabiru Shehu ‘Yanɗaki.
A lokacin zanga-zangar dai a wasu wurare musamman arewacin Najeriya an samu matsalolin fashe-fashen wurare da sace-sace da lalata dukiyoyi.
To sai dai waɗannan ƙungiyoyin sun nesanta kansu daga hakan. ”Mun rubuta musu cewa za mu yi zanga-zanga daga ƙarfe 8:00 na safe zuwa 10:00 na safe, kuma da rakiyar jami’an tsaro muka yi zanga-zangarmu, har muka ƙare su ne suka ba mu kariya”, in ji shi.
”Kuma koda muka ƙare, sai da muka kira shi jagoran hukumar DSS na jihar muka sanar masa cewa ga shi mun tashi daga zanga-zangar kamar yadda muka aiko musu a rubuce, kuma ya tabbatar mana cewa yaransa ma sun shaida masa haka”.
Ya bayyana cewa bayan sun kammala ta ne wasu ɓata-gari da ke iƙirarin zanga-zangar suka je suka aikata abin da bai dace ba.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka sanya dokar taƙaita zirga-zirga, sakamakon fargabar ɓarkewar rikici a lokacin zanga-zangar da aka fara a ranar Alhamis.