Ana takun-saƙa tsakanin manyan sarakunan Yarabawa biyu

Spread the love

A ranar Litinin ne Alaafin na Oyo Oba Akeem Owoade ya bai wai Ooni na Ife Oba Enitan Adeyeye Ogunwusi wa’adin sa’o’i 48 domin soke muƙamin sarauta na masauratar Okanlomo da ake zargin ya bai wa wani attajiri a Ibadan mai suna Dotun Sanusi, duk a ƙasar Yarabawa

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan harkokin ƴada labarai na Alaafin, Bode Durojaiye ya fitar.

Sanarwar ta ce: “Yanayin yanzu da ake ciki shi ne ya wajabta wa Alafin na Oyo ya bai wa Ooni na Ife wannan umarnin domin ya soke muƙamin sarautar da aka bai wa Injiniya Dotun Sanusi cikin sa’o’i 48 ko kuma ya fuskanci hukunci.”

Sanarwar ta jaddada cewa, Alaafin ne kawai ke da ikon bai wa kowane mutum muƙamin sarauta da ya shafi duk fadin ƙasar Yarbawa wadda kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da hakan

“Takardar muƙamin da aka gabatar wa Oba Ogunwusi lokacin da aka naɗa shi ya takaita ikon ƙarfinsa kawai ga ƙaramar hukumar Oranmiyan, wadda yanzu ta rabu zuwa ƙaramar hukuma uku da suka haɗa da Ife ta Tsakiya da Arewacin Ife da kuma Kudancin Ife.” sanarwar ta ƙara da cewa.

Har yanzu dai fadar Ooni na Ife bata mayar da martani kan wannan sanarwar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *