Ana taron masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya

Spread the love

Gamayyar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya sun shirya wani taron masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro da yankin arewacin ƙasar ke fuskanta.

Taron na kwana biyu – wanda aka shirya ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar mai ritaya – ya samu halartar manyan masu faɗa a ji daga yankin arewacin ƙasar.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da sarkin musulmin Najeriya mai alfarma Dakta Sa’adu Abubakar lll da gwamnonin jihohin Gombe da Kaduna da Zamfara Da Katsina da Bauchi da kuma Nasarawa.

Sauran manyan baƙin sun haɗar ministocin Tsaron ƙasar, Mohammad Badaru Abubakar da Mohammed Bello Matawalle, da babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, Janar C.G Musa da tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar Dakta Abubakar Bukola Saraki, da tsohon gwamnan Katsina Aminu Bello Masari, da ministan Ayyukan gona da samar da abinci da shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN, da tsohon shugaban hukumar zaɓen ƙasar Farfesa Attiru Jega.

An shirya taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro da yankin ke fuskanta.

Yankin arewacin Najeriya dai ya daɗe yana fama da matsalolin tsaro kama daga na masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa da ‘yan fashin daji da ‘yan tayar da ƙayar bayan Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *