Ana Tuhumar Dan Nijeriya Da Budurwarsa Da Zargin Kisan Kai A Kasar Zambia

Spread the love

Rundunar yan sandan kasar Zambia ta gurfanar da wani dan Nijeriya mai suna Nathaniel Barthram dan shekaru 34 da kuma budurwarsa mai suna Maria Zaloumis, a gaban kotun bisa zarginsu da kashe wani matashi mai suna Enock kasengele dan shekaru 22 a duniya.

jaridar IDONGARI.NG ta bayyana cewa, an mayar shari’a tasu zuwa babbar kotun bayan kotun majistiri ta Kabwe ta rage musu tuhumar daga kisan kai zuwa kashe mutum bada gangan ba da kuma sanya su a hannun beli.

Barthram da Zaloums suna cikin mutane biyar da ake tuhuma da aikata laifin a yankin gidan gona na, Onani Farm Kabwe, a ranar 17 ga watan augustan 2025 tare da sauran mutanen da suka hada da Daniel Chiluwa da Fortune Mwitangati da kuma Gift Daka.

Yan sandan kasar Zambia suna tuhumarsu da laifin kisan kai da farko bayan gurfanar da su a gaban kotun majistiri kamar yadda Wamundila Liswaniso ya karanto musu tuhumar.

A cewarsa ana zarginku da aikata laifin halaka Enock Simfukwe Kesengele a ranar 17 ga watan augustan 2025, wanda yin hakan ya saba da sashi na 200 na kundin dokokin kasar  Zambia.

Kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan yarin Mukobeko har zuwa lokacin da za a samu shawarwari daga ma’aikatar shari’ar kasar.

Haka zalika lauyan gwamnatin kasar Joseph Zimba, ya shaidawa kotun an saukaka tuhumar daga kisan kai zuwa kashe mutum bada niyya ba.

Lauyan dake kare wadanda ake zargin ya roki kotun ta sanya su a hannun beli, domin a cewarsa ana bayar da beli ga wadanda ake zargin ya aikata laifin kisan kai bada niyya ba, kuma za su cika dukkan sharudan da aka gindaya musu.

Kotun ta sanya su a hannun belinsu kan kudin kasar wato Kwacha dubu 20 kowannensu kwatankwacin kudin Nijeriya naira miliyan 1 da dubu 261 da 256, tare da kawo ma’aikatan gwamnatin biyu da kuma karbe fasfo din Barthram duka dai a wani bangare na sharadin belin kamar yadda jaridar  IDONGARI.NG ta ruwaito

Shari’ar ta dauki hankalin al’ummar kasar Zambia, wadda za a ci gaba da sauraron ta a babbar kotun kasar cikin makonni masu zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *