Ana tuhumar shugaban kungiyar asiri na Kenya da kashe mabiyansa fiye da 400

Spread the love

Ana tuhumar shugaban ƙungiyar asiri a ƙasar Kenya da laifin kashe mabiyansa fiye da 400.

Jagoran ƙungiyar da ke kiran kansa fasto, Fasto Paul Nthenge Mackenzie, tare da wasu mataimakansa na fuskantar tuhuma kan laifukan da suka hada da ayyaukan ta’addanci da kisan kai da garkuwa da mutane da kuma azabtar da yara ‘ƙanana a dajin Shakahola.

An gufanar da fasto Mackenzie a wata Kotu da ke Mombasa tare da kusan mutane casa’in da suka haɗa da mata da yara ƙanana da ake yi wa shari’ar kisan kai.

Da farko an zarge shi da sanya mabiyansa da suka haɗa da daina cin abinci har sai mutum ya mutu.

Tsoffin mabiyan ƙungiyar asirin sun bayyana yadda aka umarce su da fara azumin da zai kai su lahira.

Mai gabatar da ƙara ya ce ganau 400 na nan cikin shiri, inda wasu suka buƙaci bayar da shaida a sirri cikin wannana mako.

Munin al’amarin da ya faru a dajin Shakahola ya sanya yan ƙasar ta Kenya da dama buƙatar sanin abin da ya hana ‘yansanda kai ɗauki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *