Ana Zargin Jami’an Kwastam Da Yin Sanadiyar Rasa Rayukan Mutane 2 A Kano.

Spread the love

Kano

Rundunar yan sandan jahar Kano ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan wasu jamian hukumar hana fasa kwauri kwastam, bisa zarginsu da yin sanadiyar rasuwar mutane 2, a yankin garin Kadage dake karamar hukumar Gezawa a jahar.

A wannan makon ne ake zargin jami’an kwastam din , sun biyo wata mota kirar Golf, wadanda suke zargin sun dauko shinkafa yar kasar waje, wanda hakan ya haifar da rasa fasinjojin motar biyu da kuma jikkatar mutane2 .

Wani shaidan gani da ido ya ce , jami’an kwastam din ne suka biyo direban motar a guje, har sai da motar kwastam din kirar Hilux ta danne karamar motar.

Bayan faruwar lamarin ne suka yi kokarin yin kwana su gudu amma hakan ba ta samu ba, sakamakon yadda mutanen gari suka yi gaggawar kai dauki tare da kama biyu daga cikin su.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun fara gudanar da bincike kan lamari kuma za su sanar wa al’umma halin da ake ciki.

Mai magana da hukumar kwastam shiyar Kano da Jigawa , ya bayyna cewa ba jami’an shiyar ba ne , duk da cewar lamarin ya faru a jahar Kano.

To sai dai kakakin kwastam a shiya ta 2 dake jahar Kaduna SC Isah Sulaiman, ya ce tabbas mutane biyu sun rasu, bayan sun yi taho mu gama da motar jami’ansu kuma sun fara gudanar da bincike don yi wa kowa adalci.

Dokar hana shigo da shinkafa yar kasar waje ta fara aiki ne , tun lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ake zargin jami’an kwastam na wuce gona da iri yayin gudanar da aiyukansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *