Zauren kungiyar Yan jaridun kafofin sada zumuntar Facebook, wadanda Suka sanya Mata sunan ( Arewa Online journalist Forum), ta siyar da buhunhunan shinkafar da Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayar a matsayin tallafi na rage radadin halin rayuwar da ake ciki.
A cikin makon da muke ciki ne, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 109, ga kungiyar, don rage mu su raɗaɗin rayuwa musamman a watan Ramadan mai alfarma.
Rahotannin da jaridar idongari.ng, ta samu ya tabbatar da cewa an siyar da kowanne buhun shinkafa mai girman 10kg kan kudi naira dubu goma ( N10,000 ).
- Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Yar Shekaru 14 A Dakin Otal
- Kashe Wasu Jagororin Yan Bindiga Da Sojoji Suka Yi Zai Kawo Raguwar Ta’addaci: Masana Tsaro.
Kungiyar ta karbi buhunan shinkafar 109, ne a ranar Laraba a unguwar Sharada, inda aka kaita Unguwar Kabuga, sannan aka dinga sanya kananan Buhunan shinkafar biyar cikin babban Buhu, bayan an kammala ciniki ta baki daya kan kudi naira miliyan daya da dubu chasa’in.
Ana zargin an siyarwa da ita a jahar Plato, bayan an kammala ciniki kan kowanne buhu daya na 10kg, har aka tura mu su kudin ta Hanyar asusun Banki.
Rahotanni na cewa , tuni aka Kai shinkafar jahar Plato ga Wanda ya biya kudin sama da naira miliyan daya.
Wadanda suke cikin Dandalin WhatsApp na kungiyar , sun koka sosai sakamakon yar burum-burun, da aka yi mu su, ba tare amincewar su ba, wajen siyar da shinkafar da ya kamata kowannensu ya samu buhu 1.
Hajiya Fatima Dangote, ta bayar da tallafin ne, duba da halin matsin da wasu ke fama dashi, don rage mu su radadin kuncin rayuwa,amma abun takaici aka siyar da shinkafar.
Yanzu haka dai ana ci gaba da tura wadanda Suka aike da asusun bankunansu kudin shinkafar da aka siyar.
Akwai mabukata Masu Yawa da suke neman ataimaka mu su, da kayan abincin sakamakon halin kuncin rayuwar da ake ciki.
A baya dai Shugaban Kungiyar Arewa Online journalist Forum, dake jahar Nasarawa, Malam Barrah Almadany, ya mika sakon godiya ga Uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote, a madadin sauraran mambobin kungiyar, sakamakon tallafin kayan abincin da ta bayar.
Gidauniyar Aliko Dangote, ta tallafawa miliyoyin Mutane a fadin Nigeria, da kayan abinci Danye da kuma Daffafe harma da Burodi da ake rabawa a Kullum.