Ana zargin ma’aikacin bankin UBA da sace 3.3m daga asusun kwastoma a jihar Kano.

Spread the love

Ana zargin wani ma’aikacin banki da  sace Naira miliyan 3,390,000 daga asusun kwastoma a bakin United Bank Of Africa UBA dake Sharada a jihar kano.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa, wani mai suna Garzali Wada Ibrahim ne ya kai ƙorafinsa bankin, domin a saita masa manhajar da ake amfani da ita wajen tura kuɗi inda ya hadu da wani ma’aikacin banki mai suna Osaka Omada dake bangaren kula da aboka hulda, wanda ya sake saita mu sa manhajar ta wayar salula wato mobile application.

Ibrahim ya kara da Cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2023  aka fara cire masu  wasu kudade ba tare da izinin sa ba daga cikin Asusunsa har naira miliyan uku da dubu dari uku da casa’in (N 3,390,000) ta wannan manhajar dake wayar sa.

“Bayan an cire ne sai nayi mamaki kuma nayi zargin Osaka Omada na UBA din Sharada ne da yin wannan aika-aika domin babu wanda yaga lambobin sirrin cire kuɗi daga manhaja ta sai Osaka domin yana kallo na sanya” inji Garzali”.

Kashi na farko na kudaden da aka sata sun kai kimanin 2m,000,000 inda aka tura su zuwa asusun bankin WEMA mai lamba 7790847364 mai dauke da sunan BSTPOS-Musa.

Haka zalika kashi Na biyu na kudin da aka cire ya kai kimanin 1.3m  inda aka tura shi zuwa asusun Opay mai lamba 9068129712 mai suna Angela Anulika weke.


Ya kara da cewa yayi yunkurin neman haƙƙin sa domin a dawo masa da kuɗaɗen sa amma haƙan sa ya ci tura saboda haka ya bukaci Babban Bankin Najeriya ya shiga tsakanin sa da Bakin United Bank Of Africa UBA rashen Sharada dake jihar kano domin karbo masa kudinsa daga wajen ma’aikacin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *