Hukumar kwastam ta tabbatar da rasuwar wani jami’in ta mai suna Hamza Abdullahi Elenwo, akan hanyar Daura- Kano, a jahar Jigawa lokacin da suke gudanar da bincike.
Jami’in hulda da jama’a hukumar kwastam shiyar B Kaduna, Isah Sulaiman , ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Asabar.
Lamarin ya faru ne lokacin da ake binciken wata mota da ake zargin an yi fasa kaurin ta zuwa Nigeria ta barauniyar hanya, direban motar ya afkawa jami’in kwastam din dake bakin aiki, har ake zargin direban ya buge shi da motar.
Rahotanni na cewa an garzaya da jami’in zuwa babban Asibitin Kazaure daag bisani kuma aka mayar da shi FMC Katsina, inda ya likita ya tabbatar da rasuwarsa.
Kakakin kwastam shiya B, Isah Sulaiman, ya ce an kama wanda ake zargin, kuma yana hannun jami’an yan sanda a jahar Jigawa don fadada bincike a kansa.
- Jami’an Tsaro Da Fursunoni Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Mogadishu
- An sako ‘yan jaridar Kaduna da ‘yan bindiga suka sace tare da iyalansu