An garzaya da Wani limamin masallaci sashin bayar da agaji gaggawa dake asibitin Murtala Muhammed Kano, sakamakon Zargin da ake yi wa matarsa da buga masa Dutse akansa.
Lamarin ya Faru ne a yankin unguwar Zango Yar’adu’a Kwatas dake karamar hukumar Ungoggo a Jahar.
Dan uwan limamin, Mallam Zakariya, ya shaida wa idongari.ng, cewar tunda aka kawo shi, Asibiti bai San waye akansa ba.
Sai dai ya ce daman matar limamin a wasu lokutan ta kan nuna kamar akwai matsalar kwakwalwa akan ta.
Abdullahi Adamu, shi ne makoncin limamin ya shaida cewa suna cikin gida da sassafe aka fada mu su faruwar lamarin, inda suka garzaya da shi wajen jami’an Yan Sandan Zango sannan aka tafi da shi zuwa asibitin Murtala Muhammed sashen bayar da agajin gaggawa.
” Mu na kira da mahukunta da ma su Hannu da shuni su taimaka don ceto rayuwar sa.
Idongari.ng, ta Yi kokarin Jin ta bakin Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, hakan Bai samu ba.
- Amurka ta ƙaƙaba wa editocin gidan talabijin ɗin RT na Rasha takunkumai
- Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 31 tare da rusa gida 5,000 a jihar Kano