Ana Zargin  Matasa 4 Da Kashe Mai Sana’ar Achaba Da Kuma Jefa Gawarsa A Rijiya A Jigawa.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Jigawa, ta samu  kama, daya daga cikin matasan da ake zargi da aikata fashi da makami, kisan kai da kuma jefa mutum a rijiya.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa DSP Shiisu Lawan Adamu, ya ce sun karbi korafi daga wajen wani mai suna Malam Jamilu Bako mazaunin garin Duwala Tsohuwa a karamar hukumar Garki dake jahar, cewar dan sa mai suna Anas Jamilu, wanda yake yin sana’ar Achaba ya fita bai dawo ba, kuma sun bincika duk inda yakamata amma ba su samu labarinsa ba.

Bayan karbar korafin ne jami’an yan sandan su fara gudanar da bincike, inda mutanen garin suka fara jin wari yana fitowa daga cikin wata rijiya har suka sanarwa da yan sandan.

MB Talla

DSP Shisu Lawan , ya kara da cewa an shiga cikin rijiyar inda aka gano cewar mutum ne , kuma bincike ya tabbatar da cewar Anas Jmailu ne, da ake nema kuma bayan an kaishi asibiti likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Binciken yan sanda na farko-farko ya kai ga samun labarin kama daya daga cikin matasan da ake zargin mai suna Aisu Auwalu, a unguwar Yankaba dake jahar Kano, a lokacin da yake yunkurin siyar da babur din.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa ana zargin matasan da hada kai su hudu , inda mutane 2 daga cikin su suka nemi Anas din ya kai su bayan garin wajen da za su tarar ragowar mutanen da ake zargin.

Da zuwansu ne suka bukace shi ya tsaya a kusa da wata rijiya, yayin da sauran mutane biyun suka fito daga wani waje dauke da Gorori, har ake zargin sun hallakashi, sannan suka jefa shi cikin rijiyar kuma suka tafi da babur dinsa domin su siyar.

Tuni dai wanda ake zargin na farko, Aisu Auwalu, ya shaida wa yan sanda cewar sun hada kai da Babale, Sadau da kuma wani da bai ambaci sunansa ba, wajen aikata laifin kisan kai , fashi da makami da kuma jefa mutum a Rijiya.

Kwamishinan yan sandan jahar Jigawa A.T. Abdullahi, ya bayar da umarnin an dawo batun babban sashin gudanar da binciken manyan laifuka na CID, dake shelkwatar rundunar dake Dutse , inda ake ci gaba da farautar sauran mutanen da ake zargi don su girbi abinda suka shuka a gaban kotu.

Saurari sautin muryar DSP Shiisu Lawan Adamu kakain yan sandan jahar Jigawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *