Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Ofone Modupe Alasin, a karamar hukumar Efon-Alaaye da ke jihar.
Kakakin rundunar a jihar, SP Sunday Abutu ne ya tabbatar da kisan matar, inda ya ce an kama mijinta yayin da ake ci gaba da bincike.
Binciken farko-farko dai ya nuna mijin ne ya lakada wa matar tasa duka saboda ta ki zuwa gonarsu a kan lokaci.
Wani makwabcin gonar ya ce ya jiyo marigayiyar tana ihun neman taimako, amma duk da haka mijin nata ya ci gaba da nada mata na jaki.
Kazalika, wata majiya daga ’yan sanda ta ce bayan duka ne mutumin ya bukaci ta samo masa ruwa daga wani rafi da ke kusa da gona.
Sai dai a kan hanyarta ta zuywa debo ruwa a rafin, ta yanke jiki ta fadi ta mutu.