Ana Zargin Wani Dan Kasar Chaina Da Yi Wa Yar Direbansa Ciki A Kano.

Spread the love

Ana zargin wani dan kasar China mai suna Mr. Shibu, mazaunin jahar Kano, da yi wa wata matashiyar budurwa ciki na tsawon watanni shida.

Mahifin budurwar mai suna Mallam yusuf , ya kasance Direban Mr. Shibu, wanda yake aiki a rukunin masana’antun unguwar Sharada Kano.

Mallam Yusuf, ya shaida wa Alfijir Labarai, cewa gidansa da wajen da yake aiki babu nisa, shi yasa yar tasa ta ke zuwa wajen sa, inda Mr. Shibu, ya kyalla ido akanta har ya lallaba ta da sunan soyya ya dirka mata ciki.

Ita ma matashiyar budurwar ta tabbatar da hayoyin da dan kasar Chainan yabi har ya yaudare ta, har ya cimma burinsa.
Bayan lamarin ya fara bayyana ne ake zargin Mr. Shibu , ya bayar da motarsa har aka yi wa budurwar Allurai domin zubar da cikin da ta ke dauke da shi a wani asibiti amma cikin bai zube ba, sai ma galabaita da budurwar ta yi.

Rahotanni na cewa na ba wa mahifin budurwar Naira dubu hamsin da zummar suje wani asibitin a zubar da cikin kuma zai kara masa naira miliyan daya.

Bayan sunje wani asibiti mai suna Best Choice, a unguwar Sabuwar Gandu, likitan da ke kan aiki ya tabbatar mu su cewar basa yin irin wannan aikin a asibitin.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, an yi wa mahaifin budurwar barazanar rasa aikinsa matukar ya bari zancen ya fito fili, wannan dalilin ya kara jefa shi cikin damuwa kamar yadda iyalannsa suka tabbatar.

Tuni dai hukumar Hisbah ta jahar Kano ta shiga cikin maganar , inda aka gayyato bangarorin guda biyu, don aje asibiti a bincikar lafiyar Budurwar.

To sai dai Mallam Yusuf Direba, ya yi zargin hukumar ta hisbah na yunkurin daura auren dan kasar Chinan da yar tasa.
Duk kokarin da Alfijir labarai, ta yi don jin ta bakin babban kwamandan hukumar hisbah na jahar Kano Sheik Mallam Aminu Ibrahim Daurawa, ya ci tura , Haka zalika shima mukaddashin kwamandan hukumar DR. Mujahiddin Aminuddin bai samu damar daga waya da kuma sakon da aka aike masa ba kan wannan zargi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *