Rundunar yan sandan jahar Jigawa, ta samu nasarar kama wani matashi mai suna Nura Mas’ud, mazaunin garin Ma’azu a karamar hukumar Sule Tankarkar, bisa zarginsa kashe kakarsa Zuwaira Muhammed, ta hanyar zuba mata Fetur sannan ya Kyasta Ashana.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adamu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai, a ranar Asbaar 12 ga watan Oktoba 2024.
Sanrawar ta ce sun faruwar mummunan lamarin a ranar 8 ga watan Oktoban da muke ciki, a mazabar Dan Gwanki dake jahar.
Bayan faruwar lamarin ne jami’an yan sandan jaahar suka yi gaggawar matar zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwar ta kuma tuni an yi janazarta bisa tsarin addinin musulinci.
Wanda ake zargin ya shaida wa yan sanda cewa a lokuta da dama, kakar ta sa tana bayyana masa cewa, sannu da jiki shi kuma baya so amma taki daina wa, shi yasa ya dauki wannan mataki.
Binciken yan sanda na farko-farko ya tabbatar da cewa matashin da ake zargi, ya na matsalar ta kwakwalwa, inda yake karbar kulawar likitoci a asibitin kula da masu larular kwakwalwa na Kazaure.
Kwamishinan yan sandan jahar Jigawa , CP AT Abdullahi, ya bayar da umarnin zurfafa bincike kan lamarin, kafin a gurfanar da shi a gaban kotu don ya zama izina ga masu son maimaita hakan.
Saurari muryar Wanda ake zargin..
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Sabunta Sashin Karbar Korafin Mutanen Da Jami’in Dan Sanda Ya Ci Zarafinsu.
- Son zuciya ne ya haifar da koma-bayan dimokuraɗiyya a Nijeriya – Sani GNPP