Yanzu haka ana zargin wani matashi mai suna Mutawakkil Ibrahim, dan shekara kusan 30 mazaunin unguwar Kofar Dawanau, ya halaka kakanninsa biyu ta hanyar caka mu su wuka dake jihar Kano.
Wani makocin mamatan biyu Malam Mukhtar Harisu ya tabbatarwa da tashar Muhasa TV da Rediyo cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na safiyar Alhamis 25 ga watan Satumba 2025.
Matashin ya aikata wannan danyen aikin ne sakamakon zargin da shan kayan maye, ya yin da wasu kuma suka bayyana cewa matashin daman na fama da lalurar tabin kwakwalwa.
Wadanda aka halaka din sun hada da Muhammad Dansokoto dan shekara 75 da Hadiza Tasidi mai shekaru 65 dukansu mazauna birnin Kano..
Sai dai wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa, wannan bashi ne karon farko ba, da matashin ke yi wa kakannin na sa barazanar kisa , amman kuma ba su dauki wani mataki akai ba.
zuwa lokacin hada wannan rahoto mun tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kan faruwar lamarin amma ba mu samu ji daga gare shi ba, bayan mun kira shi a waya da kuma aike masa da sako.