Ana Zargin Wani Matashi Da Kashe Mahaifiyarsa A Kano

Spread the love
Daga Garin Kachako dake Ƙaramar Hukumar Takai kuwa wani matashi Umar Yunusa Kachako ake zargin ya kashe Mahaifiyar sa, ta hanyar dukanta da taɓarya a lokacin da take tsaka da barci.
‘Yan uwan matashin ne suka tabbatar da hakan a yayin zantawar su da jaridar GTR HAUSA, inda suka ce lamarin ya faru ne da Misalin ƙarfe 10 na daren ranar Talatar data gabata inda yayi amfani da Taɓarya ya raba mata kanta biyu.
Yakubu inusa Kachako shine yayan matashin da yayi wannan ɗanyen aiki ya ce babu shakka lamarin ya matuƙar gigita rayuwar su, domin kuwa bai jima da barin gidan ba aka sake kiransa kuma bayan ya dawo ya taras da ita a cikin jini shi kuma ƙanin nasa yana gefe da Taɓarya a hannu.
Toh sai dai kuma ya ce dama yana da Lalurar da aka gaza gano kanta, domin kuwa Asibiti sunce Matsala ce a Ƙwaƙwalwar sa a inda su kuma masu masu Maganin gargajiya suka ce Aljanu ne.
Haka kuma ya ce ya haura shekara 12 yana yawon nema masa Magani, ta yadda duk watan duniya sai anyi masa Allura da kuma magaungunan da yake siya masa, wanda hakan ya haddasa ƙarewar ƙarfin sa gaba-ɗaya.
Adan haka ne ya ce suna roƙon mahukuntan da su raba su da wannan ɗan uwa nasu ta hanyar kaishi gidan mahaukata ko kuma su san yadda zasu yi da shi, amma shi da dukkan ‘Yan uwansa sun sallama shi.
Akan wannan batu jaridar GTR HAUSA ta tuntuɓi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, domin jin inda lamarin ya kwana duba da ‘yan uwan Matashin suka ce yana hannun ‘yan Sandan Kachako, kuma Kiyawa ya ce bai sami labarin ba amma zai bincika kuma da zarar ya kammala tattara bayanai zai waiwaye mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *