Rundunar yan sandan jihar Kano, tabbatar da rasuwar wani matashi mai suna Sulaiman Musa, dan shekaru 25 mazaunin Garin Goda a karamar hukumar Mijinbir, sakamakon kwada masa Gora da yayan budurwarsa mai suna Mansur Umar dan shekaru 25, yayi lokacin da yaje zance wajen kanwarsa mai suna Fiddausi Umar .
Kakakin rundnar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna ne yabayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa da Muhasa TVR a ranar litinin.
Sanarwar ta ce , jami’an yan sanda sun garzaya wajen da lamarin ya faru , inda suka kai wanda aka bugawa gorar asibiti amma likita ya tabbatar da rasuwarsa sakamakon samun raunuka a sassan jikinsa.
SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa, yanzu haka wanda ake zargin Mansur Umar, yana hannun yan sanda, kan zargin kisan kai da ake yi masa.
- Ma’aikatar Yada Labarai Ta Shiryawa Masu Yada Manufofin Gwamnatin Kano A Shafukan Sada Zumunta Bitar Wuni Biyu
- An kama ɗan daba mai yin fashi a cikin shigar mata a Kano
Kwamishinan yan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin an dawo dashi babban sashin gudanar da binciken kisan kai dake Bompai kuma da Zarar an kammala za a gurfanar dashi a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.
Rundunar taja hankalin al’umma musamman wadanda suke mu’amula ta yau da kullum idan wani abu ya shiga Tsakani da al’umma kar a dauki doka a hannu ko yunkurin duka ko wani abu da makami wanda hakan yake sa rasa rayuka .
A karshe rundunar ta ce duk wani abu da ya danganci daukar makami a kaucewa masa domin gudun yin danasani.