Ana zargin wasu fursunoni 3 sun fasa gidan yarin Ijebu Ode tare da tsere wa

Spread the love

Wasu fursunoni 3 sun tsere daga gidan gyaran hali da tarbiya dake karamar hukumar Ijebu Ode a jahar Ogun.

Kakakin hukumar kula da gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya na jahar , Victor Oyeleke ne, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta a ranar Talata.

Ya ce wadanda suka tsare din sun lalata shingen tare fasa ginin ,sannan suka samu hanyar guduwa.

ya kara da da cewa yanzu haka an shiga farautar daurarrun su uku da ake zargi da fasa gidan yarin.

Victor ya ce suna da na’urar tantance bayanan su, da kuma nambar yan uwansu domin tuntuba , kuma suna aiki da sauran hukumomin tsaro dan ganin an cafke su nan da dan lokaci kankani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *