An ga ƙarin jami’an tsaro a fadar sarkin Kano da ke Ƙofar Kudu a yau Juma’a.
Hakan ya kawo cikas ga zirga-zirga da shige da fice a cikin fadar mai ɗimbin tarihi, inda Sarki Muhammadu Sanusi II ke da zama.
Za a iya ganin jami’an tsaro da kuma motocin tarwatsa masu zanga-zanga waɗanda aka jibge a fadar.
Bayanai sun nuna cewa a yau ne aka tsara cewa Sarki Muhammadu Sanusi II zai yi wa ɗaya daga cikin masu riƙe da sarauta mafi girma a masarautar, Wamban Kano, Mannir Sanusi rakiya zuwa Bichi domin kama aiki a matsayin hakimi.
Sai dai jibge jami’an tsaron ya janyo cikas ga faruwar hakan.