Rundunar sojin Najeriya ta sanar da yau 27 ga watan Maris a matsayin ranar da za a yi jana’izar sojoji 17 da aka kashe a garin Okuama da ke jihar Delta.
Rundunar ta ce za a yi jana’izar ne a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ƙarfe 3 na yamma agogon Najeriya.
Hakan yazo ne ƴan makonni bayan wasu ɓatagari sun kashe wasu daga cikin sojojin da ke aiki ƙarƙashin runduna ta 181 da aka turo domin kwantar da tarzomar da ke tsakanin al’ummar garin Okuama da Okoloba na jihar da ke kudu maso kudancin Najeriya.
Shugaban ƙasa Bola Tinibu da ƴan Najeriya da dama sun yi allahwadai da kisan sojojin.
- Dole a riƙa ɗaukan ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda – Tinubu
- Jami’an Tsaro Sun Gaiyace Ni Domin Amsa Wasu Tamboyoyi Cikin Girmama Wa: Sheikh Gumi
Shugaban ƙasar ya umarci rundunar da ta tabbatar cewa waɗanda suka aikata kisan sun fuskanci hukunci.
A hoton da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X, sojojin da aka kashe sun haɗa da :
- Lt Col AH Ali, kwamandan runduna ta 181
- Manjo SD Shafa
- Manjo DE Obi
- Kyaftin U Zakari
- Staff Sajant Yahaya Saidu
- Koporal Yahaya Danbaba
- Koporal Kabiru Bashir
- Lance Koporal Bulus Haruna
- Lance Koporal Sole Opeyemi
- Lance Koporal Bello Anas
- Lance Koporal Hamman Peter
- Lance Koporal Ibrahim Abdullahi
- Private Alhaji Isah
- Private Clement Francis
- Private Abubakar Ali
- Private Ibrahim Adamu
- Private Adamu Ibrahim