Jam’iyyar APC reshen mazaɓar Ganduje da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dakatar da shugaban jam’iyyar naa ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje nan take.
Jaridar intanet ta Solace Base ta rawaito cewa mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a a mazaɓar Ganduje ne Haladu Gwanjo ya sanar da dakatar da shugaban jam’iyyar a wani taron manema labarai da aka yi a Kano ranar Litinin.
Gwanjo ya bayyana cewa matakin dakatar da Ganduje daga jam’iyyar ya faru ne saboda zargin da gwamnatin Kano take masa na aikata rashawa da wadaƙa da kuɗaɗe.
- Gwamnan Jahar Naija Ya Ba Wa Jami’an Tsaro Umarnin Harbe Yan Daba.
- Hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris
A cewarsa, mambobin jam’iyyar sun yanke shawarar dakatar da shugaban APC na ƙasa ne bayan ƙuri’ar yanke ƙauna da aka kaɗa a kan shi saboda gazawarsa wajen wanke sunansa daga tarin zarge-zargen da aka yi masa na rashawa da cin hanci.
Zarge-zargen dai sun haɗa da wani bidiyo da aka yi ta yaɗawa wanda a ciki ake zargin sa da karɓar cin hanci daga ɗan kwangila.
Gwanjo ya bayyana cewa matakin ya fara aiki daga yau ɗin nan – 15 ga watan Afrilu.