Hukumar zaɓen jihar Kaduna ta ayyana jam’iyyar APC mai mulkin jihar a matsayin wadda ta cinye zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 23 da kansilolin jihar 255 da aka gudanar yau Asabar.
Shugabar hukumar zaɓen jihar, Hajiya Hajara Mohammed ce ta bayyana haka a ofishin hukumar ɗazu da maraice.
Galibi dai dama zaɓukan ƙananan hukumomi jam’iyyun da ke mulkin jihar ne ke lashe duka zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli.
Wani abu da masana ke kallo a matsayin barazana ga dimokraɗiyya, sakamakon zargin kura-kurai da ake yi wa zaɓukan.
To sai dai gwamnan jihar Satana Uba Sani, yayin kaɗa ƙuri’arsa a rumfar zaɓen da ke ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa ya kore wannan zargi, inda ya kira zaɓen jihar a matsayin ”ingantacce kuma sahihi” da ya gudana ba tare da wata tangarɗa ba.
A nata ɓangare babbar jam’iyyar hamayyar jihar PDP ta yi iƙirarin rashin gudanar da zaɓen a jihar.