Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya ce yankin arewa ba cima-zaune ba idan ana maganar tattalin arziki.
Ndume ya bayyana haka ne a wata sanarwa, inda ya ce kowace jiha ko yanki da ke ƙasar na buƙatar wani domin ci gaba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Sanatan ya ce, “yankin Arewa ba zai taɓa zama cima-zaune ba ko mai dogaro da wani yankin saboda muna da arziki.
“Waɗanda suke tunanin wai waɗannan ƙudurorin harajin arewa zai shafa, ba su fahimta ba ne. Dukkan wani mai ƙaramin samu a ƙasar sai lamarin ya shafe shi.”