Arzikin Ɗangote ya ninka zuwa dala biliyan 28 bayan fara aikin matatar mansa

Spread the love

Hamshaƙin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote ya samu ƙaruwar arziki, inda dukiyarsa ta ninku a sanadiyar fara aikin matatar mansa.

Yanzu arzikin attajirin ya ninku zuwa dala biliyan 27.8, kamar yadda rahoton mujallar ‘Bloomberg Billionaire Index’ – mai nazarin masu arziki na duniya – ya nuna.

Matatar man ta Ɗangote, wadda aka buɗe a jihar Legas da ke kudancin Najeriya, ita ce irinta na farko, wadda ke iya tace kusan kowane nau’in ɗanyan mai.

Matatar za ta iya kawo gagarumin sauyi a ɓangaren tattalin arzikin Najeriya, ta hanyar mayar da ƙasar mai dogaro da kanta a ɓangaren man fetur.

Game da ƙalubalen da ya fuskanta wajen gina matatar, Dangote ya ce ba zai yi wa ko da babban maƙiyinsa fatan shiga irin damuwar ba.

”Ban san muna gina wani abu ba ne da zai zo ya dame mu,” in ji Ɗangote mai shekara 67 a wata ziyara da ya kai New York.

“Matsalolin sun zo daga ɓangarori da dama, mutane da yawa suna ta ruɗar da mu cewa ba za mu iya ba, kuma ko da mun yi ɗin, ba za mu samu nasara ba,” kamar yadda kafar Bloomberg ta ruwaito.

Tun bayan da matatar ta fara aiki a watan Janairu, an samu saɓani daban-daban tsakaninta da gwamnati da kuma kamfanin man fetur na ƙasar, da kuma amfaninta ga ƴan ƙasa da ma tasirinsa ga muhalli.

A wajen Dangote – wanda ya fara zama biloniya da kasuwancin siminti – buɗe matatar man wani gagarumin aiki ne a rayuwarsa.

Gina matatar ya ɗauki shekara 11, ta kuma ci dala biliyan 20, kuma mafi yawancin aikin, shi ya ɗauki nauyinsa.

Yanayin kasuwancin Dangote

Ɗangote, wanda ya fara furfura yanzu saboda shekaru, hamshaƙin ɗankasuwa ne.

Asalin kasuwancinsa na kayayyakin masarufi ne, yawanci siminti ne da sukari da gishiri da fulawa.

Arzikinsa abin ban mamaki ne kasancewar a ƙasar da yake, kashi 40 na mutanenta suna rayuwa ne cikin talauci, kuma yawancin arzikin ƙasar a man fetur ne.

Sai dai a ɓangaren buɗe matatar man, ya shiga matsaloli.

An ƙwace asalin wurin da ya so ya buɗe matatar, bayan ya sha fama da rikice-rikice da ƴan ƙauyen.

Daga baya sai ya koma kudancin jihar Legas, inda can ma ya fuskanci wasu ƙalubalen da mutane.

Bayan an ba shi sabon filin, sai ya kasance kwari ne, inda dole ya yi aikin yashewa sannan ya yi ciko na kusan ƙafa biyar (mita 1.5) domin kiyaye aukuwar ambaliya. Kamfanin ya gina dam da tashar jirgin ruwa domin aikin matatar.

Shekara biyu bayan fara ginin, sai annobar korona ta ɓarke.

Wasu daga cikin kamfanonin da suke kawo masa kayayyaki sai suka samu matsalar kuɗi, suka dakata.

Sannan a wani ɓangaren kuma, Ɗangote yana biyan dala miliyan 50 zuwa dala miliyan 60 duk shekara a matsayin kuɗin ruwa na bashin dala biliyan 5.5 da ya karɓa daga bankunan cikin gida.

Amma bayan buɗe matatar a bana, dole ta fara neman ɗanyen mai daga ƙasashen Turai, wanda wannan ya ƙara masa tsada.

A yawancin harkokin kasuwancinsa, Ɗangote yana samun alaƙa mai kyau da shugabannin Najeriya, wanda hakan ke taimakon harkokinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *