Asibitin kwararru na Best Choice ya rage kaso 30 cikin 100 a ayyukan kula da hakora

Spread the love

 

A wani bangare na tausaya wa da kyautatawa al’umma da shugaban asibitin Best Choice Alh Auwal Lawal yayi ya bayyana rage kaso 30 cikin 100 na aikin kula da aikin hakora, asibitin a wata tattaunawarsa da jaridar Alfijir labarai

Lawan ya jaddada cewa, sabon sashin kula da hakoran zai duba mara sa lafiya ne a kan wannan ragi tare da ba su shawarwari duba da yanayin da ake ciki na sanyi

Daga nan Auwal ya jaddada bukatar dake akwai ga duk wadanda ke fama da matsalolin hakora cewa, asibitin yayi tanadin abubuwan da suka dace game da ƙwararrun likitocin haƙora da suka goge tsawon shekaru, da kuma isassun kayan aikin haƙora na zamani.

Ya jaddada kudirinsu na share hawayen marasa lafiya inda ya bukace su da kada su yi sanya wajan cin gajiyar wannan tagomashi na ragi da aka samar don kula da lafiyar baki da ta hakori.

Idan za a iya tunawa, asibitin ya koma babbar helkwatarsa ta dindindin dake shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, dake kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

Ya kara da cewar baya ga ficen da suka yi a fannin kula da mafitsara, asibitin na aiwatar da muhimman ayyukan da suka hada da jinyar kananan yara (Paediatrics), tiyata (surgery), kula da masu tabin hanka( psychiatry), bangaren hakora (Dentals), gashin kashi ( physiotherapy) sashin kula da cutukan mata (Gynaecology) da bangaren masu kula da masu ciki da haihuwa, bangaren fata (dermatology), manyan dakin gwaje-gwaje, kantin magani, da sashin kula da jarirai.

Lawan ya tabbatar da cewa asibitin cike yake da na’urorin kiwon lafiya na zamani irin na kasashen duniya, ga kuma tsayayyiyar wutar lantarki 24-7.

Hakazalika asibitin bashi da wani reshe ciki ko wajen Kano, mazauninsa na dindindin na shatale-talen Tal’udu kusa da Kwalejin Bashir El-rayya, dake kan titin Aminu Kano anan birnin Dabo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *