Samar da magunguna da kula da marasa lafiya a cikin Kananan Asibitocin dake kusa da Al’umma zai temaka wajen rage cinkoso a Manyan Asibitocin Jihar kano.
Bayanin hakan ya fito ta bakin Mai Unguwar Darma Malam Ashiru Hamza lokacin da Kungiyar Darma Zumunta suka kai katin Rubuta Maganin zuwa karamin Asibiti dake Unguwar Darma .
Ashiru Hamza ya ce babu shakka Samar da Katin zai temakawa marasa lafiya, tare da rubuta musu magani a hukumance, inda ya bukuci Kungiyar da su kara kaimi wajen Samar da Hasken Wutar Lantarki a Asibitin.
Tinubu ya bayar da umarnin buɗe iyakokin Najeriya da Nijar
Da yake nasa Jawabin shugaban Kungiyar Darma Zumunta Alh Dan Babannan Musa Wanda ya samu wakilcin Musa Ahmad Husaini ya bayyana cewar sun himmatu wajen temakawa Marasa lafiya, da kulla zumunci da Juna, ta hakan ne suka dauki gabarar Samar da Katin a Asbitin.
Shima a nasu bangaran Likitan dake kula da Asibitin na Unguwar Darma Musa Ibrahim Buhari, ya tabbatar da cewa aikin da sukeyi yana bukatar temakon Al’umma, musamman wajen karo kayan aikin, da kula da lafiyar Asibitin…