Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya sake ɓara dangane da matsalar tsaro da ke ci gaba da addabar Najeriya sakamon ƙarin samun yawan hare-hare da ƴan bindiga ke yi.
Atiku dai ya bayyana rashin jin ɗaɗinsa musamman dangane da garkuwar da aka yi da ƴan jarida da alƙalai da shugabannin ƙwadago da iyalansu a baya-bayan nan.
Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya wanda ya bayyana damuwa a shafinsa na X, ya ce ” a wannan lokutan na tashin hankali, ƴan jaridarmu su ne ke haska wa al’umma, kuma ba sa yin ƙasa a gwiwa wajen tabbatar da jagorori sun yi abin da ya kamata. Sai dai kuma abin takaici yanzu su ne ababan kai wa hare-hare.”
A bayanin nasa da ya wallafa, Atiku Abubakar ya kawo jerin lokutan da aka yi garkuwa da mutanen da yake nuna ɓcin ransa a kai.