Atiku ya nemi gwamnatin Tinubu ta yi bayani kan bashin dala biliyan 3.3 da NNPC ya ciyo

Spread the love

Jagoran adawar Najeriya Atiku Abubakar ya ce ya kamata gwamnatin shugaba Tinubu ta fito ta yi wa ‘yan Najeriya bayani kan bashin dala biliyan 3.3 da kamfanin mai na ƙasar NNPC ta ciyo da nufin farfaɗo da darajar kudin ƙasar.

A shekarar da ta gabata ne Kamfanin mai na ƙasar NNPC ciyo bashin domin taimakawa wajen farfaɗo da darajar naira a kasuwar musayar kuɗaɗe.

To sai dai a cikin wata sanarwar da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya fitar, ya ce wani abin mamaki shi ne har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da lamarin, kuma bayanan kawai da ake samu kan batun, ana samun su ne ta wasu majiyoyin da ba na hukuma ba daga kamfanin.

Rundunar yan sandan Kano ta shirya tsaf don bayar da cikakken tsaro a ziyarar Uwar gidan shugaban kasa Oluremi Tinubu.

Yansanda sun kama mutanen da ake zargi da safarar ƙananan yara a Abuja

”An ƙulla yarjejeniyar ce da nufin biyan kuɗin da man fetur, wanda aka ƙulla da bankin ”African Export-Import” kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Atiku Abubakar ya ce abin da suka gano shi ne a yanzu Najeriya na haƙo gangar mai miliyan 1.38 a kowace rana, kuma daga cikin ƙa’idojin yarjejeniyar bashin akwai batun cewa Najeriya za ta riƙa bayar da ganga 90,000 a kowace rana da nufin biyan bashin, daga 2024 har zuwa ganga miliyan 164.25 da za a kammala biyan bashin da shi.

”To a nan ne matsalar take, domin kuwa abin da Najeriya ta tsara za ta riƙa sayar da kowace gangar mai a shekarar 2024 shi ne dala 77.96”, in ji Atiku.

”Ka ga idan aka lissafa wannan kuɗi da miliyan 164.25, kuɗin zai kama dala biliyan 12, a kan wannan ne muke son gwamnati ta fito ta yi mana bayanin yadda yarjejeniyar take”, in ji jagoran adawar ƙasar.

Sanarwar ta ce abu ne da hankali ba zai iya ɗauka ba, a ce gwamnatin tarayya za ta karɓo bashin dala biliyan 3.3 da kuɗin ruwa na kashi 12, amma ƙiyasin abin da za a biya a ce ya kai dala biliyan 12.

Wannan na nufin cewa an samu bambancin dala biliyan bakwai tsakanin abin da ke rubuce a takarda da abin da yake a zahiri.

Atiku Abubakar ya ce akwai tambayoyin da ‘yan ƙasar ke buƙatar sanin amsarsu game da yarjejeniyar, kan haka ne muke buƙatar gwamnatin tarayya ta fito ƙarara ta yi bayaninsu.

”Don haka muke kira a madadin ‘yan Najeriya, gwamnatin tarayya ta amsa mana waɗanna tambayoyi”.

1. Shin gwamnatin tarayya ce ta ƙarbo bashin?

2. Shin bashin na daga cikin basussukan da majalisa ta amince wa gwamnati?

3. Su wane ne a cikin yarjejeniyar bashin, kuma wace rawa za su taka a yarjejeniyar?

4. Waɗanne ne ƙa’idojin bashin, ciki har da wanda ya ciwo shi, da yadda za a biya, da kadarar da aka ajiye don ƙulla yarjejeniyar, da kuma kuɗin ruwa?

5. Daga ƙarshe, kuma me ya sa wani kamfanin Bahamas ke cikin yarjejeniyar?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *