Bidzina Ivanishvili, tsohon firaministan Georgia, ya yi alƙawarin bai wa tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar kyautar fan miliyan 8.4 bayan sun yi bajintar doke Portugal a gasar Euro 2024.
Georgia wadda tsohon ɗan wasan Faransa Willy Sagnol ke jagoranta, ta baje Portugal ne a jiya Laraba domin samun gurbi a zagayen ‘yan 16, inda za su buga da Sifaniya.
Ivanishvili wanda ya kafa jam’iyyar Georgian Dream kuma ya zama firaminista a 2012, ya ce nasarar a kan Portugal “abar tarihi ce kuma wadda aka daɗe ana buri”.
Attajirin ya kuma ce zai ba wa tawagar ƙarin fan miliyan 8.4 (Lari miliyan 30 kuɗin ƙasar) idan suka sake doke Sifaniya.
A ranar Lahadi ne Georgia za ta fafata da Sifaniyan a filin wasa na Cologne da ke Jamus da misalin ƙarfe 8:00 na dare agogon Najeriya da Nijar.