Auren ɗan shekara 63 da ‘yar 12 ya harzuƙa mutane a Ghana

Spread the love

Wani hamshaƙin ɗan gargajiya mai shekara 63 ya fusata jama’a a Ghana bayan ya auri wata yarinya ‘yar shekara 12.

Bokan Nuumo Borketey Laweh Tsuru XXXIII, ya yi auren ne a wani bikin al’ada da aka yi ranar Asabar.

Sakamakon caccaka ne kuma, shugabannin al’umma suka fito suna cewa mutane ba su fahimci al’adun gargajiyarsu ba.

Mafi ƙarancin shekarun aure bisa doron doka a Ghana shi ne 18 kuma an samu raguwar yawan auren wuri a ƙasar, amma lamarin na ci gaba da faruwa nan da can.

A cewar wata ƙungiya Girls Not Brides, mai rajin kawar da auren wuri, kashi 19% na ‘yan matan ƙasar ne aka yi musu aure kafin su kai shekara 18.

Bidiyo da hotunan gagarumin shagalin bikin na ranar Asabar wanda gomman jama’ar yankin suka halarta, sun karaɗe shafukan sada zumunta, lamarin da ya harzuƙa da yawan al’ummar Ghana.

A lokacin bikin, matan da suka yi jawabi a harshen Ga sun faɗa wa yarinyar ta riƙa yin shiga don hilatar mijinta.

Ana kuma iya jin su lokacin da suke ba ta shawarar ta shirya wa shiga rayuwa irinta matar aure kuma ta yi amfani da turarurrukan da suka ba ta kyauta wajen tayar wa mijinta sha’awa.

Irin waɗannan kalamai ne suka harzuƙa mutane, don kuwa ana ganin hakan na nuna cewa aure ne na haƙiƙa ba kawai na bidiri ba.

Masu sukar lamarin sun yi ta kira ga hukumomi su rusa auren sannan su gudanar da bincike a kan Mista Tsuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *