Auren Dolen Da Ake Shirin Yi Mun Ne Ya Sanya Ni Bankawa Mutane Wuta A Kano: Shafi’u Abubakar

Spread the love

Matashin saurayin nan da ake zargi da kunna wa mutane wutar, a lokacin da suke gudanar da sallar Asuba a cikin masallaci , a yankin garin Gadan dake Karamar hukumar Gezawa, ya bayyana cewa ya yi hakan ne sakamakon auren dole da ake so yi masa.

Wanda ake zargin mai suna Shafi’u Abubakar , mai shekaru 38 a duniya , ne ya bayyana hakan ne lokacin da ya tattauna wa da jaridar idongari. ng, a Ranar Laraba.

Ya Kara da cewa matsalace tsakaninsa da Wata yar uwarsa , da ake son aura masa ita , kuma baya son auren da ake son mu su, har hakan ya bata masa rai ya dauki wannan mataki.

“Auren dole za a yi mun , idan ba na dole ba me zai mutum ya sa wuta domin ba na sonta cewar, Shafi’u Abubakar”.

Shafi’u Abubakar, ya ce ya shaida mu su tun abaya cewar baya so , amma Suka ki yadda , kuma mahaifin budurwar kanin mahaifinsa ne.

Matashin ya tabbatar da cewa, a baya ya taba dukan kanin mahaifin NASA a kofar Masallaci.

” Gaskiya idan akan wannan Abu ne ba Zan yi nadama ba”.

Idan ba a manta ba, Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta tabbatar da cafke matashin mai suna Shafi’u Abubakar, bisa zargin sa da kunna wa mutane bayan ya zuba Fetur, lokacin da suke sallar Asuba.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a Ranar Laraba.

Sanarwar ta ce sun samu kiraye-kirayen jama’a kan cewar wuta ta tashi da misalin karfe 5:20am na Asubashin Ranar Laraba, a wani masallaci dake kauyen Gadan Karamar hukumar Gezawa, a daidai lokacin da suke yin sallar Asuba, wadanda mutane da dama Suka samu ranuka.

Bayan samun rahotan ne Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tura wasu jami’an yan sanda , wadanda Suka kware kan duk wani Abu da yake tashi kamar Abun fashewa da dai sauransu, karkashin jagorancin CSP Haruna Isma’il, da kuma Baturen yan sanda na Gezawa CSP Haruna Iliya, tare da ba su umarnin a gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru, dan ganin an yi abunda yakamata.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa, bayan sunje wajen ne , aka samu nasarar toshe ko’ina ,tare da gaggauta ceto mutane 24, inda aka garzaya da su Babban asibitin Murtala Muhammed, a Birnin Kano.

Rahotanni na cewa an kwantar da mutane 24, da Suka hadar da Manya guda 20 da kuma yara hudu.

  • Binciken yan sanda na farko-farko, ya tabbatar da cewar, an jefa wutar ce ta Hanyar amfani da man Fetur.

Kakakin yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yanzu haka Wanda ake zargi na farko mai suna Shafi’u Abubakar, an Kama shi, kuma ya tabbatar da cewa shi ne yaje ya siyo man Fetur a gidan mai, sannan ya sanya a cikin Wata roba ya watsa a cikin masallacin ya kunna wuta, ta dalilin haka hannayensu biyu Suka kone.

Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya faru ne sakamakon rigimar cikin gida ta rabon gado, kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a sanar da al’umma halin da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *