Ba batun harajin Tinubu ba ne ya janyo ɗauke auren ‘yar Sanata Barau daga Kano’

Spread the love

Iyalan gidan marigayi Ado Bayero sun musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta cewa sun ɗauke bikin ɗauren auren ‘yarsu, Maryam Nasir Ado Bayero da ɗan mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Jibrin (Abba) Barau I Jibrin, saboda dambarwar da ta biyo bayan gabatar da ƙudurin harajin Shugaba Tinubu da aka yi a majalisar.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin tsare-tsaren bikin, na ɓangaren iyalan amarya, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi, Sarkin Dawaki Babba na Kano, ya fitar a jiya Litinin, ya ce an sauya wajen ɗaurin auren ne, daga Kano zuwa Abuja, ba don tankiyar da ƙudurin harajin ya janyo ba.

Ya ce kamar yadda al’adarsu ta tanada, aihakin iyayen amarya ne zaɓar rana da wajen da za a ɗaura aure ba iyayen ango ba.

Ya ƙara da cewa tun makonin da suka gabata aka sauya wajen ɗaurin auren da za a yi ranar Juma’a 13 ga watan nan na Disamba, domin sauƙaƙa wa manyan baƙin da suka nuna sha’awarsu ta halarta daga sassan ƙasar da kuma waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *