Ba gudu ba ja da baya kan ficewarmu daga Ecowas’

Spread the love

Shugabannin gwamnatin mulkin soji a Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun ce ba zasu koma ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin yammacin Afirka, Ecowas ba.

Shugabannin uku sun gana a karon farko, domin ƙulla wata haɗaka da za ta fuskanci ƙalubalen da suke fuskanta daga ƙasashe maƙwabtan su.

A tsakanin 2020 zuwa 2023 sojoji suka ƙwace mulki a Mali da Burkina Faso da kuma Nijar, a wata guguwar juyin mulki da yankin ya yi fama da ita.

Dukkan ƙasashen uku da ke ƙarƙashin ƙawancen na Alliance of Sahel States suna fama da rikicin ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi, wanda kuma yana daga cikin dalilan da sojojin suka ce sun tilasta masu ƙwace mulki.

Da yake jawabi a wajen taron ƙasashen uku a Nijar, shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ce ƙasashen sun yanke shawarar kafa wata haɗaka da za ta kula da muradun jama’arsu, ba tare da shisshigin ƙasashen waje ba.

”Za mu samar da gamayya ta zaman lafiya da taimakon juna da kuma kawo ci gaba a bisa mutumta al’adunmu na Afirka.” Inji Jana Tchiani.

A cikin watan Janairu ƙasashen suka sanar da shirin su na ficewa daga Ecowas, wadda itama za ta gudanar da taron ta a ranar Lahadi.

Janar Tchiani ya yi jawabin ne a gaban takwaransa na Burkina Faso’s, Kaftin Ibrahim Traoré da kuma na Mali, Kanal Assimi Goïta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *