Ba mu ƙayyade farashin naira 600 kan kowacce litar mai ba – Dangote

Spread the love

Shugabannin da ke kula da matatar man Ɗangote sun yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa an ƙayyade farashin man fetur a kan naira 600 kan kowacce lita, inda ta bayyana rahotannin a matsayin jita-jita marar tushe.

A wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin kasuwanci da sadarwa na kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar a shafin sada zumunta na X, ya yi tsokaci kan jita-jitar da ake ta yaɗawa da ke cewa matatar ta na tattauna wa da ƙungiyar dillalan man fetur ta ƙasar IPMAN, a kan yadda za a cimma matsaya wajen sayar da man a kan naira 600 kan kowacce lita.

Kamfanin ya fayyace cewa bai ƙulla wata alaƙa da ƙungiyar ta IPMAN ,ya kuma jaddada cewa duk wani mataki da kamfaninsu ko matatar da ɗauka za a sanar a hukumance.

Sanarwar ta cewa “An jawo hankalinmu kan labarin da jaridar Punch ta wallafaa da ke cewa kamfanin Dangote ya ƙayyade farashin man fetur kan naira 600 kan kowace lita, a jiya Talata, 13 ga watan Agustan 2024.”

“Za mu so mu fayyace cewa ba mu da ta wata alaƙar kasuwanci da IPMAN a yanzu.”

Ya ce “Ba mu taɓa tattaunawa kan farashin man fetur da IPMAN ba kuma ba su da wani hurumin yin magana a madadinmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *