Ba Mu Amince A Saki Nnamdi Kanu Ba : CNG

Spread the love

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Nigeria, CNG ta yi watsi da kiran da tsagin marasa Rinjaye na majalisar Wakilai suka yi, na neman a saki, Nnamdi Kanu shugaban haramtacciyar kungiyar masu neman ballewa da Fafutukar kafa Kasar Biyafara IPOB.

Kungiyar ta bayyana bukatar a matsayin cin zarafi ga wadanda ake zargin ayyukan Kanu ya shafa da sauran al’ummar Najeriya, Inda gwamnatin Najeriya ta kama tare da tuhumar Kanu kan ayyukansa.

A cikin wata sanarwa da CNG ta fitar mai dauke da sa hannun Babban Jami’inta na kasa, Comared Jamilu Aliyu Charanchi, ya tunasar da irin abubuwan da Kanu ya aikata a baya, inda ta ce ta kai kararsa ga Majalisar Dinkin Duniya a ranar 7 ga watan Agusta, 2017, kan ayyukan kungiyarsa, da suka yi zargin na ta’addanci ne, kuma gwamnatin Najeriya a hukumance ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ta’addanci a ranar 27 ga watan Yuni, 2021, biyo bayan kama Kanu da kuma tuhume-tuhume da suka shafi tada tarzoma, barnata dukiya, da kuma mutuwar ‘yan Najeriya da dama da jami’an tsaro.

Chiranci ya bayyana matukar kaduwarsa yadda yan majalisar wakilai, ke goyon bayan a saki Kanu, wanda ake tsare da shi bisa umarnin wata kotun da ke da hurumi.

Daga karshe ya yi Kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye wajen yin watsi da irin wannan matakin kuma kar su Lamunci duk wani abu da zai Ta’azzar ko kawo wanzuwar ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *