Ba mu amince da wasu mombobin kwamitin albashi ba – Shugaban NLC

Spread the love

Shugaban kungiyar Kwadago na Najeriya, Joe Ajaero ya ce wasu gwamnonin da har yanzu ba su fara biyan albashi mafi karanci na naira 30,000 na daga cikin ‘yan kwamitin da gwamnatin tarayya ta kaddamar domin sake yi duba kan sabon albashi mafi karanci.

A ranar Talata ne dai mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin mai mutum 37 domin yin duba ga tsarin albashi da kuma fito da sabon tsarin albashi mafi kankanta.

Yan bindiga sun sake sace wasu ‘yan mata ‘yan gida daya a Abuja

Wutar Lantarki Ta Kashe Barawon Taransufoma

To sai dai shugaban kungiyar ta Kwadago, Joe Ajaero da yake tattaunawa a gidan talbijin na Channels ya ce “wasu daga cikin ‘yan kwamitin musamman ma gwamnoni har yanzu ba su cika alkawarin biyan albashi mafi kankanta ba. Saboda haka ina fatan sun shiga wannan sabon kwamitin da zuciya daya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *