Ba Mu Bari An Zalinci Kowa Ba Ko Tayar Da Tarzoma: AIG Muhammed Usaini Gumel

Spread the love

Tsohon Kwamishinan yan sandan jahar Kano, AIG Muhammed Usaini Gumel, ya godewa al’ummar jahar, bisa goyon baya da hadin kan da suka ba shi tsohon shekara daya da Wata 1 da kwana 22 da ya Yi a matsayin Kwamishinan yan sanda.

AIG Muhammed Gumel, ya bayyana hakan ne, a wajen wani kwarya-kwaryar taro da aka shirya don bayar da nambobin girmama ga wasu daga cikin Jami’an yan sandan da sauran al’umma da suke bayar da gudunmawa a harkar Tsaro.

” Rana ce da na ke mika godiya ta ga al’ummar jahar Kano, da sauran mutane baki daya kamar gwamnati, yan kasuwa, Malaman addinai da kuma shuwagabannin mu wato sarakuna iyayen kasa” AIG M.U. Gumel“.

Ya kuma godewa ya jaridu da sauran hukumomin tsaro tare da yan uwa da abokan arziki, a tsawon lokacin da ya dauka na shekara daya da Wata 1 da kwana 22 a matsayin Kwamishinan yan sandan Kano 45.

AIG Gumel, ya ce hakika wannan tafiya ce mai tsaho wadda ta hadu da tangarda iri-iri, tun daga lokacin da aka Fara kawo shi a matsayin Wanda zai jagoranci Tsaro a zaben gwamna na shekarar 2023, har zuwa bayan lokacin da aka sanar da sakamakon zaben dama Shari’ar da aka Yi har zuwa kotun koli, yan sanda da sauran hukumomin Tsaro wadanda Suka tsaya tsayin daka Suka tabbatar ba su ba wa jama’a Kano kunya ba.

” Ba mu Bari an zalinci wani ba, ba mu Bari an tayar da tarzoma ba, ba mu Bari an tayar da zaune tsaye ba” AIG M.U.Gumel”.

A bangare guda kuma ya ce , sun Yi tsayin daka wajen gano dalilan da suke sanya matasa shiga harkar Daba, akan haka ne aka tsawatar mu su , tare da Kai sintiri a wurare daban-daban na kwaryar birnin Kano, kuma Kama sama yan Daba 2,000, wadanda tuni aka gurfanar da su a gaban kotu.

Jarida Idongari.ng, ta ruwaito cewa , AIG Gumel, ya yi matukar kokari ta fuskar  daidaita al’amuran da suka shafi tsaro a jahar duk da kalubalen da ya fuskanta, ciki harda  zargin da ake yi wa wasu na  goyon bayan matasa da suke  aikata laifin fadan daba da kwacen wayoyin al’umma.

Kimanin watanni 9 kenan da kakkabe aiyukan fadan daba, da kwacen wayoyin jama’a, bisa jajircewarsa da kuma addu’o’in al’ummar jahar.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *