Ba mu ce ba za mu goyi bayan Tinubu ba – ACF

Spread the love

Ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa, ACF, ta ce rahotannin da ake yaɗawa cewa ta yanke shawarar wanda za ta goya wa baya a zaɓen 2027 ba haka ba ne.

Wasu kafofin watsa labarai a Najeriya ne suka ruwaito cewa ƙungiyar bayan taronta, ta ce ba za ta mara wa shugaban ƙasa Bola Tinubu baya ba.

BBC ta tuntubi Farfesa Tukur Baba, wanda mai magana da yawun ƙungiyar ne, wanda ya ce, “Gaskiya ƙungiyar tuntuba ba ta ce haka ba. Mun fitar da bayani da muka karanta a gaban ƴan jarida na bayan taro, inda muka ce ƙungiyar ta gamsu ta fito fili ta bayar da shawarwari da kuma yin bayani kan inda arewa ta nufa. Sai muka ce akwai abubuwa da ya kamata mu yi a game da halin da ƙasar take ciki, sai muka ga abin da ya shafi arewa shi ne rashin tsaro da taɓarɓarewar tattalin arziki wanda muka ga ya fi shafar ƴan arewa.”

Farfesa Baba ya ƙara da cewa, “Mun ga wasu matakai da wannan gwamnati ta ɗauka suna ƙara kawo koma-baya ga zamantakewa musamman ma na tattalin arzikin arewa.”

“Sannan mun buƙaci gwamnati ta gyara inda ta nufa a wajen gyara tattalin arziki. Mun ce ba shakka tattalin arziki na son gyara, amma a yi gyaran ta yadda mutane ba za su tagayyara ba domin kada magani ya zo ya fi ciwo zafi. Don haka muka kira gwamnatin tarayya ta sake duba abin da take yi, ta tabbatar da cewa mutane ba su tagayyara ba.”

Farfesa Baba ya ƙara da cewa an samu ci gaba a ɓangaren ilimi a yankin arewa, amma ana buƙatar ƙari.

“Idan ka koma shekarar 2950, a arewa masu digiri ba su wuce biyu ba, haka aka zo lokacin da aka samu ƴanci, nan ma ba su wuce su 10 ba. Amma yau babu wata ƙaramar hukuma da ba za ka samu yaro da ya je jami’a ba.”

Sai dai ya ce akwai buƙatar gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki a yankin arewa su bayar da gudunmuwa domin ƙara inganta harkokin ilimin yankin.

“Muna kira ga gwamntoci da duk wani ɗan arewa a duk inda yake ya taimaka wajen inganta ilimi. Ba gwamnati ba ce kaɗai za ta yi aikin. Kowa zai iya taka rawarsa, ko dai mutum ya ɗaukar nauyin karatun wani ko ka gyara makaranta ko faɗakar da iyaye a kan muhimmancin ilimi,” in ji farfesa Tukur Baba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *