Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin masarautu da ke faruwa a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu a ranar Lahadin da rundunar ta wallafa a shafin sada zumuntarta naX.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umurnin hana Gwamna Abba Yusuf mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.
Kotun ta kuma dakatar da aiwatar da sabuwar dokar da ta soke masarautun Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano.
Duk da umarnin kotun, gwamnan jihar, Abba Yusuf, ya mayar da Sanusi a matsayin sarkin Kano, yana mai cewa “alkalin da ya bayar da wannan umarni ba ya cikin Najeriya a lokacin ba ya bayar da umarnin”.
“Saɓanin ra’ayin kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano kamar yadda jaridar Premium Times ta buga a ranar 26 ga Mayu 2024, sojojin Najeriya ba su da hannu a rikicin masarautar Kano kuma ba su da hannu wajen aiwatar da wani umarnin kotu. Sun dauki matakin ne kawai don duba duk wata matsala ko zagon kasa da za a iya samu a rikicin masarautar Kano.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Batun da ya fi ɗaukar hankalin sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro shi ne hana tabarbarewar doka da oda a jihar”
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gano Shirin Yin Kone-kone Cikin Dare A Wasu Muhimman Wurare Don Haifar Da Rudani.
- Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gano Shirin Yin Kone-kone Cikin Dare A Wasu Muhimman Wurare Don Haifar Da Rudani.
Rundunar sojin ta ce za ta shiga tsakani ba tare da ɓata lokaci ba idan aikin tabbatar da tsaro na neman ya fi ƙarfin ‘yan sanda.
“Duk abin da Sojoji ke yi a wannan mataki shi ne sanya ido kan lamarin da kuma kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana idan lamarin ya ta’azzara da zai kawo barazana ga tsaron jihar da ma yankin baki daya.” in ji sanarwar.
An sake nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan sauke shi daga karagar mulki da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sake nada shi a makon da ya gabata, bayan amincewa da kudurin dokar masarautar jihar Kano na 2024 wanda aka gyara da majalisar ta amince a kai.
Tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje dai ya sauke Sanusi daga muƙaminsa a ranar 9 ga Maris, 2020 bayan zargin sa da almundahana da kuɗain masarauta da kuma rashin biyayya.
Danbarwar Masarautar Kano: Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano a Kotu
Wata Kungiya Ta Bukaci Sarki Aminu Ado Ya Bar Kano Don Wanzar Da Zaman Lafiya