Ba mu muka hana Hafsat Chuchu kin yin Magana agaban kotu ba: Barista Haruna Magashi

Spread the love

Lauyan dake kare Hafsat Surajo, ( Chuchu) barista Haruna Magashi, ya musanta zargin da ake yi kan cewar su ne suka hana ta yin magana, a lokacin da aka karanto mata kunshin tuhumar aikata laifin kisan kan abokin kasuwancin ta mai suna Nafi’u Hafiz, a gaban babbar kotun jahar Kano.

Tun a ranar 21 ga watan Disamban 2023, ne ake zargin Hafsat Surajo da caccaka wa Nafi’u wuka a sassan jikinta wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwarsa.

A zaman kotun na ranar Alhamis an karanto wa Hafsat kunshin tuhumar har sau bakwai amma taki yin Magana.

Barista Magashi ya shaida wa jaridar Idongari.ng,cewa zargin da ake yi suna da hannu wajen hanata yin Magana, ya ce basu ne suka umarce ta, ta yi gum dab akin ba.

Idongari.ng facebook link https://www.facebook.com/profile.php?id=100089819831293

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ƴan kasuwar da ke ɓoye kayan abinci

Nan ba da jimawa ba farashin kayan abinci zai sauka: Tajudeen Abbas

Ya kara da cewa zargin da jama’a suke yi mu su, ba za a iya hana su ba, domin suna da hakki yin zargi, kuma mutum ya dauki ra’ayin da yake so.

Magashi ya ce matukar akwai tabbatarciyar Magana kuma tana da ahalinta yan jaridar da suke zuwa kotun, su yakamata su bayyana wa al’umma abinda ya faru.

Jaridar Idongari.ng, ta ruwato cewa, jami’in kotun Bashir Bello Fagge, ya karanto wa Hafsat Surajo kunshin tuhumar aikata laifin kisan kai ta hanyar caccaka wa Nafi’u wuka a sassan jikinsa, karkashin sashi na 221 na dokar kasa, har sau bakwai ana karanta mata inda ki yin Magana.

Da farko mai shari’a Zuwaira Yusuf , ta ce adan jinkirta sakamakon Hasat Surajo, ta yi gum da bakin ta ko wani abune ya hanata yin Magana,kuma bayan an dawo an sake karanta mata tuhumar , nan ma taki cewa komai.

Lauyar gwamnatin jahar Kano, Barista A’isha Mahmud, ta roki kotun akai wadda ake tuhumar ta farko asibiti domin a duba kwakwalwarta sakomakon kin cewa komai da ta yi.

Mai shari’a Zuwaira Yusuf , ta bayar da umarni ga likitan dake gidan gyaran hali da tarbiya na Goron Dutse , ya binciki lafiyar kwakwalwar Hafsat Surajo, sakamakon kin yin Magana bayan karanto mata kunshin tuhumar har sau bakwai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *