Ba mu da labarin buhun siminti ya kai 15,000 a Kasuwa : Fatima Dangote

Spread the love

Shararen dan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana damurwa kan yadda tsadar Dala ke kara hauhawar farashin kayayyaki, inda ma su karafin ke kara fadawa cikin damuwa.

Yar shahararren dan kasuwar, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ita ce ta bayyana hakan, bayan kammala taron sada zumunci da Dangote Group ya yi da Yan Jarida na Arewacin Nigeria,a jiya Laraba, wanda aka gudanar a birnin Kano.

Hajiya Fatima Dangote, ta ce sun jima da siyar da kamfanin fulawarsu ga Kamfanin Olaf, domin Fulawa, Taliya da Samobita ba sune suke yi ba a yanzu kusan shekaru biyar kenan da siyar da kamfanin.

Sai dai ta kara da cewa, bisa yarjejeniyar da suka yi da kamfanin shi ne za su ci gaba da yin amfani da sunansu zuwa wani lokaci, kuma nan da shekara guda yarjejeniyar za ta kare.

Ta ce yanzu abunda kamfanin Dangote Group, ya ke yi sune gishiri, Sikari, Siminti sai kuma shinkafa wadda za su fara a cikin wannan shekara ta 2024.

Gwamnati za ta ƙara yawan mutanen da za ta bai wa tallafin kuɗi

Gwamnatin Binuwai Ta Ba Wa Makiyaya Wa’addin Ficewa Daga Jihar

Fatima Dangote, ta mayar da martani kan yadda ake samun tsadar farashin kayan kamfanin Dangote, in ta ce kayan da suke sarrafa wa, siyo su ake yi daga kasashen ketare kuma da Dala ake amfani wajen siyan shiya sa farashin yake karuwa idan Dala ta tashi.

A bangaren tsadar farashin siminti, ta ce sun zauna da gwamnatin tarayya, kuma sun cimma matsayar cewar farashin sa ba zai haura naira dubu bakwai zuwa dubu takwas ba.

Fatima ta ce mahaifin ta ya jima ya gudanar da aiyukan alkairi, domin kyautata rayuwar al’ummar jahar Kano, da kuma makotansu shi yasa a wannan lokacin ya kudiri aniyar tallafa wa mabukata da kayan abinci sakamakon halin kunci da matsin rayuwar da ake ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *