Ba Mu Da Masaniyar Sunayen Tsofaffin Gwamnonin 58 Da Aka Fitar Saboda Almundahana: EFCC.

Spread the love

Hukumar yaki da ma su yi wa tattalin arzikin zagon kasa, EFCC ta nesanta kanta daga wani rahoto da ke yawo a kafafen yada labarai na cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake bincika kan zargin almundahanar kudade.

Shugaban Hukumar EFCC , Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya fitar a matsayin martani a kafafen yada labaran dake yada labarin da bashi da tushe balle Makama.

Hukumar EFCC ta Kara da cewa, Sam ba ita ce ta, fitar da jerin sunayen gwamnoni 58, da ake zargin su lakume sama da naira Tiriliyan 2.187, a shekarun da suka shafe suna jagoranar jahohinsu.

Hukumar ta shawarci al’umma da su yi watsi da labarin sunayen tsofaffin gwamnonin da aka gani suna yawo a kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *