Babban hafsan sojin ƙasa a Najeriya, Janar Taoreed Lagbaja ya jaddada ƙudurin rundunar soji na kare martabar dimokraɗiyyar ƙasar.
Da yake yi wa mahalarta taron ƙarawa juna sani kan aiki da hedikwatar rundunar ya shirya a Abuja, Janar Lagbaja ya ce rundunar ba ta da burin yi wa dimokraɗiyyar ƙasar maƙarƙashiya.
Ya yi kira ga sojojin ƙasar su ci gaba da ba da himma wajen gudanar da ayyukansu.
Alƙawarin da Janar Lagbaja ya ɗauka na zuwa ne sakamakon yunƙurin da aka yi na kifar da gwamnati a yankin Afirka ta yamma da tsakiyar Afirka da suka fuskanci aƙalla juyin mulki bakwai cikin shekara huɗu da ta gabata.
Gwamnatin Enugu ta kashe kaji 30,000 a yayin rusau
Malaman Kano sun sasanta Abba Kabir da Sheikh Daurawa
Mali da Guinea da Burkina Faso sai a baya-bayan nan Nijar – dukkansu mambobin ECOWAS sun fice daga ƙungiyar cikin shekaru huɗu da suka gabata.
Chadi da Sudan da ba sa yankin Afirka ta Yamma suma sun fuskanci juyin mulki a 2021.