Ba mu dakatar da Osimhen daga tawagar Najeriya ba – NFF

Spread the love

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta musanta rahotonnin da ke cewa ta ɗauki matakin ladaftarwa kan ɗan wasan gaba na Super Eagles Victor Osimhen sakamakon kalaman da ya yi a kan tsohon mai horarwa Finidi George.

A ranar Lahadi ne wani bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta inda a ciki tauraron ɗan wasan na Najeriya ya ce “ya daina girmama Finidi” saboda an ce ya soke shi game da ƙin taka wa ƙasarsa leda a wasannin neman shiga Kofin Duniya da aka yi mako biyu da suka wuce.

Sakataren hukumar Nigeria Football Federation (NFF), Mohammed Sanusi, ya ce ba su da wata niyyar hukunta Osimhen kan kalaman nasa.

“NFF ba ta ba da umarnin ɗaukar wani mataki ko kuma daddalewa kan dakatar da ɗan wasan daga tawagar Najeriya ba,” in ji shi cikin wata sanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *