Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ce ba ya nadamar cire tallafin man fetur da ya yi a farkon kama mulkinsa.
Tinubu ya bayyana haka ne a tattaunawarsa ta farko da kafafen yaɗa labaru tun bayan hawa mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi masa tambaya kan ‘ko da ya fi kyau idan an jinkirta cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar naira’.
Tinubu ya ce “babu yadda za a yi na bari ana sayar da man fetur ta yadda ƙasashe maƙwafta za su riƙa samun garaɓasa. Ba na nadamar komai game da cire tallafin man fetur.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, sa’ilin jawabin karɓar mulki ne Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur.
Masana da dama na kallon cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar naira a matsayin abubuwan da suka ta’azzara matsalar tattalin arziƙi da al’ummar ƙasar suka faɗa ciki.