Ba ni da masaniya kan sakin Murja Kunya – Gwamna Abba Kabir

Spread the love

Gwamnatin jihar Kano ta ce ba ta da masaniya kan sakin fitacciyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature, ya shaida wa BBC cewa gwamna Abba Kabir ba shi da masaniya kan kama ita Murja.

”Ba mu da masaniya kan wa ya saki Murja, bangaren shari’a ne zai iya ba da bayani kan haka,’’ in ji Sanusi Bature.

Ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf ba ya shiga harkar da ta shafi bangaren shari’a.

Kakakin gwamnan ya ce batun bai kai wani al’amari ba da zai kai ga gwamnati ta saka baki.

Ana azumi kan tsadar rayuwa a jihar Borno

Shari’ar Murja Kunya: Hukumar Hisbah a Kano ta musanta labarin da ake yada wa kan murabus din kwamandan ta Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

”Mai girma gwamna ba ya nan ya tafi hutu, kuma bai kamata a alakanta shi da wannan karamin al’amari ba,” in ji Sanusi Bature.

Ya ce girman kujerar gwamna ta fi a alakanta ta da batun saboda mutum sama da miliyan 20 yake mulka a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *