Ba ni da masaniyar biyan masu sa ido a zaɓe $6m da Emefiele ya yi

Spread the love

Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha, ya ce bai san batun wata takarda ba da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, CBN, Godwin Emefiele ya yi amfani da ita wajen biyan sama da dalar Amurka 6.2 miliyan ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a ranar Talata.

Tsohon sakataren gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar mista Emefiele, ya ce a tsawon shekarun da ya yi yana rike da wannan muƙamin ba shi da masaniya kan takardar.

Kafar yaɗa labarai a cikin ƙasar, channel TV ta ce mista Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

Kotu ta tisa keyar Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali a Kano

Hukumar Hisbah ta jahar Kano ta Cafke Murja Ibrahim Kunya

Tsohon sakatren gwamnatin tarayyar ya kuma shaida wa kotun cewa babu ruwan gwamnatin tarayyar da biyan masu sa ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.

Mista Emefiele na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari’ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.

Ana zargin tsohon shugaban na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.

Masu sa ido a babban zaben ƙasar da aka yi a shekarar 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *