Ba za mu amince lauyoyin Birtaniya su yi aiki a Najeriya ba – NBA

Spread the love

Shugaban ƙungiyar lauyoyin Najeriya ,NBA Yakubu Maikyau, ya ce kungiyar ba za ta bari lauyoyin Burtaniya su yi aiki a Najeriya ba.

Wannan dai na da nasaba da rattaba hannun da ake zargin gwamnatin Najeriya da Birtaniya suka yi a kan yarjejeniyar kasuwanci da zuba jari ta ETIP.

Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa babban lauyan ya bayyana cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar ba tare da amincewar NBA ba, yana mai cewa kungiyar za ta ci gaba da adawa da duk wata yarjejeniya da za ta kawo cikas ga dokar ƙasar.

“Wane ƙoƙari ne gwamnatin Najeriya ta yi don ganin lauyoyin Najeriya sun sami damar yin amfani da yanayin doka a Birtaniya? Abin da ya fi ban takaici shi ne yadda aka kulla yarjejeniyar ba tare da shigar da ƙungiyar lauyoyin ƙasar kan rubutun yarjejeniyar ba,” inji shi.

Yan sandan Legas sun kama mutum 400 da ake zargi da aikata laifuka

Kotu ta yanke wa mutumin da hukumar Hisbah ta kama tare Murja Kunya hukunci a Kano.

Maikyau ya kuma buƙaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya kafa dokar ta-baci a cikin tabarbarewar tsaro da ya addabi kasar.

Yayin da yake kira ga Gwamnatin Tarayya da ta dauki kwararan matakai na magance matsalar rashin tsaro, Maikyau ya ba da shawarar saka hannun jari ga jami’an tsaro a kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *