Rundunar sojojin ƙasa a Najeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga jihar Delta ba har sai an zaƙulo waɗanda suka kashe sojoji 17 a baya-bayan nan.
Kwamandan runduna ta shida da ke aiki ƙarƙashin rundunar ko ta kwana a yankin kudu maso kudancin Najeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam ya bai wa shugabannin yankin Neja Delta tabbacin cewa sojoji za su nuna ƙwarewa wajen nemo mutanen da ke da hannu a kisan gillar da aka yi wa sojojin.
Ya bayyana haka ne lokacin da shugaban hukumar raya yankin Neja Delta Chif Samuel Ogbuku ya kai masa ziyara a hedikwatar rundunar da ke barikin sojoji a Patakwal.
Rundunar sojin cikin sanarwar da ta fitar ranar Alhamis ta ruwaito manjo janar Abdussalam na cewa nauyin da aka ɗora wa sojojin shi ne su gano makaman da ɓata-garin suka ƙwace daga hannun sojojin da aka kashe tare da tabbatar da cewa an kama duka masu hannu a kisan gillar.
Ya ƙara da cewa sojoji za su ci gaba da kasancewa a jihar har sai an cimma ƙudurin da aka sa gaba na binciko waɗanda suka tafka aika-aikar.
Diphtheria Ta Yi Ajalin Yara 4 A Kano
Chushen kudi: Dimokuradiyyar Najeriya Na Cikin Hatsari — Bugaje