Ba za mu bi umarnin gwamna ba kan batun Aminu Ado – Ƴan sanda

Spread the love

Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano, Usaini Gumel ya ce ba za su bi umarnin gwamna Abba Kabir Yusuf kan batun fitar da Aminu Ado daga gidan sarki na Nasarawa.

Mai magana da yawun ‘yansandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar wa da BBC hakan ta wayar tarho.

Kwamishinan ‘yansandan ya ce “fitar da Aminu Ado daga gidan sarki na Nasarawa zai zama kamar wuce gona da iri ne.

Usaini ya ce gwamnatin ta Kano da ta bayar da umarnin, ita ce kuma ta shigar da kara a wata babbar kotun jihar kan umarnin fitar da Aminu Ado, shari’ar da za a fara zama a a kai ranar Litinin, 24 ga watan Yuni.

‘Idan muka bi umarnin, zai kasance kamar muna yin aikin kotu ne saboda ba mu san me zai faru a kotun ba,” in ji Gumel.

An dai tsaurara matakan tsaro a fadar ta Nasarawa wajen da Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune.

A ranar Alhamis ne dai, gwamnan Kano ya bayar da umarnin fitar da Sarkin Kano na 15 daga gidan sarki na Nasarawa, inda ta ce za ta rushe da sake ginda katangar gidan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *